Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN ta ce ba za ta raka faston Ikilisiyar Omega , Johnson Suleman hukumar SSS ba domin gaiyatar nashi ne shi kadai.
Hukumar SSS ta gaiyaci shugaban ikilisiyar Omega Fire Johnson Suleman da ya halarci ofishinta yau Litini domin bada bayanai akan kalaman da yayi na ingiza wa da umurtan mabiyansa da su kashe duk wani Fulani makiyayi da ya shigo harabar iklisiyarsa.
Suleman Johnson yace ya fadi hakanne domin nema ma kansa kariya akan fulanin da suke neman kawo masa hari.
Mataimakin shugaban kungiyar (CAN) Olasupo Ayokunle ya ce kungiyar CAN din na goyan bayan Faston domin a ra’ayinsu bashi da laifi ko kadan, amma kungiyar ta ce baza ta raka faston ofishin hukumar SSS ba saboda shi kadai hukumar ta gaiyata.
Bayan haka gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya gargadi hukumar SSS din da kada su kuskura su ce za su tsare Fasto Suleman domin yana da labarin cewa ana mishi bita da kulle ne domin a tsare shi a hukumar SSS din.
Fayose yace idan har akayi hakan to zai iya kawo yakin addini a kasa Najeriya.