Ba za mu iya cewa ko Atiku zai iya shiga ko bazai iya shiga kasar Amurka ba – Gwamntin Amurka

1

Gwamnatin kasar Amurka ta ce ba za ta iya sanar da mutane matsayin shiga da fitan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kasar Amurka ba yanzu saboda dokar kasar ta hana fadin hakan ba tare da izinin wanda abin ya shafa ba.

Gwamnatin ta ce a dokar kasar Amurka, hukumar shiga da fitan kasar ba za ta iya ba da bayanai akan wani ba face alkalansa sun ba da umurnin ayi hakan saboda haka ba za su iya cewa komai ba akan hakan sai sun sami umurnin hakan daga shi kanshi Atiku Abubakar.

Wannan gidan Jarida PREMIUMTIMES ta bukaci kakakin tsohon mataimakin shugaban kasan da ya samar mata da wannan takardu domin samun bayanai akan hakan. Har yanzu bai ce komai akai ba.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya zargi tsohon mataimakin shugaban kasan cewa ba zai iya zuwa kasar Amurka din ba a dalilin hana sa shiga da gwamnatin ta yi.

Share.

game da Author