Zaharaddeen Sani babban jarumi ne a farfajiyar fina-finan Hausa domin kuwa a cikin shekaru 3 ya zama wani sananne wajen ma’abota finafinan a yankin Arewa.
An fi sanin sa da fitowa a Fina-finan a matsayin mugu ko kuma a mare mutunci inda yake nuna karewa da kuma jarumtarsa a hakan.
Gidan jaridar Premium Times ta yi hira da jarumin a Abuja inda ya fede mata biri har wutsiya akan yadda ya zama shahararren dan wasan fina-finan hausa, dangartakarsa da abokan aikinsa da kuma bangaren rayuwar soyayarsa.
Zaharaddeen Sani yace tun yana yaro yake kaunar kallon fina-finan kuma tun da ga lokacin yake sha’awar zama dan wasan fim.
Yace haduwarsa da Ali Nuhu ke da wuya sai mafarkinsa ta zamo gaskiya inda ya fara saka shi a fim dinsa na farko.
PT: Menene zumuntarka Ali Nuhu?
Ali Nuhu maigidana ne wanda ya taimaka mini wurin share mini fagen zama abin da na zama a yau. A yanzu haka ina daya daga cikin membobin kamfaninsa na FKD Records.
Ya kuma ce yana da kyakkyawar dangartaka tsakaninsa da Adam A Zango domin kuwa barci ke rabasu.
“Kodayake da farko mun dan sami rashin jituwa wanda ya girgiza farfajiyar fina-finan hausa din amma duk wannan a baya ne saboda Shaidan ne ya shiga Tsakaninmu.”
PT: Wani fim dinka ne kafi So?
‘‘Daga ni sai ke’’ Ya ce a wasan ya fito ne a matsayinsa na irin yaran attajirannan wanda basu da tarbiya ko kadan.
Bayan haka gidan jaridar Premium Times ta tambaye shi akan ‘yan wasan da su ka fi burgeshi.
Zaharaddeen Sani yace Ali Nuhu da Adam A Zango ne jarumansa a farfajiyar finafinai.
Yace dalilin hakan kuwa shine domin nuna kwarewan su akan aikinsu da yadda suke yin abin kamar dashi aka haifesu. “Abin gwanin ban sha’awa.”
A Mata kuma Zaharaddeen ya ce Fati Washa da Jamila Nagudu ne ke burgeshi kuma gwanayensa.
Zaharaddeen ya ce yana da Aure da ‘ya’ya biyu mata duk da ya so ya auri wata Jaruma a farfajiyar finafinan Hausan amma Allah baiyi ba.
Ya ce ba zai Iya fada mana sunanta ba amma haryanzu yana kan muradinsa idan Allah ya sa matarsa ne zai aure ta domin ya na sonta har yanzu.
Zaharaddeen Sani ya shaida mama cewa ya gama aikin wata sabuwar fim da zai fito mai suna ‘Dini Boy’ kuma shi bashi da niyar barin aikin fina-finan cewa ko da ya tsufa ne zai cigaba.
Jarumi Zaharaddeen ya ce ya na hutawa ne ta hanyar zama da lyalansa, yakan buga kwallon kafa kuma ya na motsa jiki.
Da muka tambaye shi akan jita-jitan da ake yi cewa ‘yan fina-finan hausa wai suna aikata ludu da madugo sai ya karya ta hakan in da ya ce yace;‘yan fina-finan Hausa mutanen kirikine da suke neman halak dinsu. Ya ce hassadace kawai amma babu irin hakan a farfajiyar.
Daga karshe ya yi magana akan koran da aka yi wa Rahama Sadau, inda yace abin da akayi mata ba muzgunawa bane horo ne akayi mata domin ta karya doka Wanda koda shine ko wani ya karya doka dole a hukuntashi. Amma ya ce shi dan wasa ne ba mai kula da shirya wa ko tabbatar da an bi doka bane. Saboda wanda hakkin hakan ke hannunsu ne suke tabbatar da hukuncin akan duk wanda ya karya doka KO da shine Ko wani.
Karanta hirar a shaffinmu na turanci a www.premiumtimesng.com