A shekarar 2016 farfajiyar fina-finan hausa ta sami kasaitacciyar cigaba da bunkasa wajen ganin ta gamsar da masu kallo.
Duk da irin wadannan nasarori da aka samu, Farfajiyar finafinan ta gamu da wadansu matsaloli wanda wannan gidan jarida PREMIUM TIMES ta zabo guda biyar cikinsu kuma ya jawo cece kuce da yawan zantattuka akai, wa ya Allah tsakanin yan wasan ne ko kuma abin da ya faru a farfajiyar finafinai din.
Gasu:
1. Koran Rahama Sadau daga cikin farfajiyar fina-finan hausa
Kungiyar ‘Motion Pictures and Practitioners Association of Nigeria MOPPAN ta kori wata jaruman fina-finan hausa wato Rahama Sadau domin ta fito a wani bidiyon wakar soyayya na wani mawaki mai suna Classiq
Duk da haka ba ta karaya ba domin bayan ta bar farfajiyar fina-finan Hausa yan zu hakan tana kasar Amurka in da ta amsa gayyatan shahararren mawakinnan mai suna Akon da kuma fitowa a wani fim da ake shirya wa a can kasar Amurkan.
2. Ludu da madugo a farfajiyan fina-finan Hausa
A watan Agusta ne aka zargi wasu jaruman ‘yan fina-finan Hausa inda har Adam Zango ya yi rantsuwa da Kur’ani mai girma cewa shi ba dan ludu bane a wani shirin gidan talabijin na Desmims. Shi kuwa Naburasaka ya yi nasa rantsuwar ne a shafinsa na Instagram.
Duk da haka malaman musulunci da kuma mazauna garin Kano da Kaduna sun yi tir da irin wannan rade-radi.
3. Rashin jituwa tsakanin Rahama Sadau da Nafisa Abdullahi
Rahama da Nafisa tun farko basa shiri da juna su ammarashin jituwar nasu ya fito karara ne a wannan shekaran akan wace ta fi kwarewa a harkar fina-finan Hausa.
Nafisa ta ce a ra’ayinta koran da MOPPAN ta yi wa Rahama Sadau bai dame ta ba ko kadan domin kowa ta kanshi yake saboda lokacin da kungiyar ta dakatar da ita a shekaran 2013 bawanda ya ce uffan akan nata. Sannan ta na ganin Rahama Sadau za ta iya daukar abin tunda ita ya shafa.
4. Sanarwan Adam .A. Zango na barin farfajiyar fina-finan Hausa.
Adam .A. Zango ya yi wata furicin barin farfajiyar fina-finan hausa a karshen shekaran nan a shafin sa na Instagram inda ya roki gafaran magoya bayansa, darektocin fina-fian hausa, masu kirkiro fim da abokan aikinsa cewa dalilin barinsa shine yana so ya koma wa rera wakoki da kuma rawa zuwa na dan wani lokaci.
A bin da ya fada ya zama abin magana kwarai da gaske a Farfajiyar finafinan amma da ga baya Adam yace ba barin farfajiyar fina-finan hausa zai yi kwatakwata ba hutu ne kawai zai je.
5 – Zargin da akayi wa hukumar tantance finafinan Hausa na Kano akan nuna wariya da nuna son kai akan finafinan da ake mikawa gaban ta domin tantancewa.
Masu shirya finafinai a wani lokaci cikin shekara ta 2016 sun yi zanga zangar lumana akan zargin nuna fifiko akan wasu fina-finan ba tare da kwakwaran dalili ba.