Jami’an tsaro sun tasa keyar wani kansila da aka kama yana siyar da buhuhunan shinkafa sama da 300 na yan gudun hijra a jihar Borno.
Kansilan mai suna Umar Ibrahim yace shugaban karamar hukumar Mafa ne ya sa shi ya siyar da shikafar ga wani mutumi Umar Ibrahim mai shagon sai da kayan abinci da ake kira Bolori Stores da wani shima mai suna Umar Salisu akan naira 8,500 kowani buhu.
Ko da yake shi shugaban karamar hukumar Mafa din Shettima Maina ya gudu sauran suna hannun Hukumar EFCC na jihar.
Ita dai wannan shinkafa wata kungiyace mai zaman kanta ta kasar Denmark mai suna Danish Refugee Council, DRC, suka agaza yan gudun hijra da shi.