2017: Kiwon Lafiyar ‘yan kasa shine muka sa a gaba sannan mun tsaro manufofi domin ganin samun nasarar hakan – Inji Ministan Kiwon Lafiya

0

Gidan jaridar Premium Times ta yi hira da ministan kiwon lafiya Isaac Adewole inda ya bada cikakken bayanai akan shirin da gwamnatin Buhari ta yi akan inganta kiwon lafiyar mutanen kasa da samar da wadataccen cibiyoyi domin kula da lafiyar jama’a da ya hada da cutar tarin fuka, cutar shan inna da bayanai akan kasafin kudin bara da na bana musamman a wannan fanni.

MATSALOLIN MA’AIKATAN KIWON LAFIYA

Da farko ya yi magana akan barazanar yajin aikin da kungiyar likitocin Najeriya suke yi sannan Ya kuma yi bayani akan albashin ma’aikatan kiwon lafiya da ba a biya ba inda ya ce gwamnati ta amince da ta biya bashin albashin ma’aikatan da suke bi tun a watan Nuwamba zuwa watan Disemban shekara 2016 nan da yan kwanaki masu zuwa.

Ya kuma ce gwamnati ta gama shiri domin gyaran asibitocin kasarnan. Ya ce gwamnati ta ware kudade har biliyan 11.7 domin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko kuma akwai shiri na hadin gwiwa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu domin samun tallafi.

Ya kuma yi bayani akan wasu ma’aikatan asibitocin jihar Akwa Ibom wanda suka yi watani har 3 ba albashi, yace wannan kuma matsalace da ake fama da shi a kasar domin a lokacin da ya yi magana da shugaban kasa akalla jihohi 24 ne suka kasa biyan albashin ma’aikatansu.

Ya ce akwai wani tsarin da ake yi yazu domin samar da inshorar kiwon lafiya ga ma’aikatan.
Bayan haka kuma Adewole yace basu da ikon tilasta wa wata jiha domin ta biya albashin ma’aikatan ta saidai za su iya rokonsu alfarma akan haka.

MATAKAI DA MA’AIKATAN KIWON LAFIYA ZA TA DAUKA DOMIN CIMMA BURINTA

Matakan da ma’aikatan kiwon lafiya za ta dauka domin cimma burinta shine kara gyara shirye shiryen ta wanda ya hada da kula da kiwon lafiyar talakawa wanda zai tabbatar da cewa talaka ya sami ingantacciyar kiwon lafiya a sauwake ba sai bashi da lafiya sannan ya fara guje-gujen neman kudin da zai biya a asibiti ba.

Sannan kuma za’a gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko saboda mutane su daina zuwa manyan asibitoci akan kananan cututtuka kamar zazabin cizon sauro, kwalera dai sauran su.

MATSALOLIN DA AKA YI TA FAMA DA SHI AKAN CUTAR SHAN INNA

Minista Adebowale ya koka da yadda cutar shan inna ta dawo wasu jihohi a kasannan musaman yankin arewa maso gabas duk da cewa ayyukan Boko Haram ne ya dan hana aii an hakan yayi wata asiri. Ya kara da cewa an tabbatar da cewa yanzu babu cutar Shan Inna a jihohin Kano, Sokoto, Ibadan da Abuja.

DOKAR KIWON LAFIYA

Ministan yace domin tafiyar da ayukkansu yadda ya kamata za su ba da bayanai yadda suka kashe kudaden da gwamnati ta ware musu a kasafin kudin bara da na bana.

Sannnan za su wallafa shi a gidajen jaridu da ta yanar gizo.

GYARAN CIBIYOYIN KIWON LAFIYA

Ya kuma ce a matsayinsa na likita so yake gwamnati ta saki kudin da fanin kiwon lafiya ke bukata domin samun nasarorin da ma’aikatan ke da burin cimma.

Ya kara da cewa a shekaran bara babban bakin kasa ta ba ma’aikatan kiwon lafiya bashin kudi da ya kai biliyan 140.

Ya ce a yanzu hakan Hukumar PEPFAR na tallafawa kananan hukumomi 2 kasa Najeriya domin kawar da cutar kanjamau, ita ma hukumar DFID na tallafawa domin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a yankin arewacin Najeriya, EU ta dauki nauyin gyara cibiyoyin kiwon lafiya 774 a jihohi 3 a wannan shekaran.

CUTAR TARIN FUKA

Ya ce a wannan shekara gwamnati za ta yi kokarin binciko masu dauke da cutar tarin fuka domin su fara shan magani tun da wuri kuma za tayi hakan ne ta hanyar sayo naurorin gwaji wanda suke nuna cutar a jikin mutum da wuri kafin ya ci jikinsa.

CUTAR ZAZZABIN LASA

Minista Adebowale ya yi kira ga mutane da su ankare da wannnan cuta na zazzabin Lassa sannan ya shawarci mutane da su gaggauta zuwa asibiti muddun suka kamu a ko wani iri zazzabi ne a jikinsu.

CUTAR KWAKWALWA

Ya ce a yanzu haka suna kan aiki akan yadda za su fito da manufofi domin shawo kan cutar musamman a yakin arewa maso gabas.

Share.

game da Author